Home / Labarai / AN RUSHE MAJALISAR ZARTASWAR JIHAR KANO

AN RUSHE MAJALISAR ZARTASWAR JIHAR KANO

 

DAGA IMRANA ANDULLAHI

A kokarin Gwamnayin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na ganin an mika ragamar mulkin Jihar a hannun zabbiyar Gwamnati, Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje da ake yi wa lakabi da Gandun aiki ya bayar da umarnin kowa ne kwamishina da mai ba Gwamna shawara ya ajiye mukaminsa domin tabbatar da muka mulki Salim alum a jihar.

A cikin wata takarda mai taken “Mika Madafun iko” da ta fito daga ofishin sakataren Gwamnatin Jihar Kano, mai dauke da da hannun Babbar sakatariyar Ofishin Hajiya Bilkisu Shehu Maimota.

Kamar dai yadda takardar ta kunsa cewa Kwamishinoni da masu bayar da shawara tare da shugabannin ma’aikatun Gwannati da kuma kamfanoni mallakar Gwannatin Jihar duk su mika ayyukan ofisoshin da suke rike da su ga manyan ma’aikatan da sune masu mafi girman mukamai ofishinsa suka ajiye aikin.

Takarda ta bayyana cewa ayayin da wa’adin mulkin gwamna Ganduje ya zo  karshe a karo na biyu, ranar 29 ga watan Mayu Shekarar 2023,kundin tsarin Mulki ya Umarce shi da ya sauke dukkan ‘Yan Siyasa masu rike da mukaman gwamnatin Jihar duk su ajiye aikin su.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.