Daga Imrana Abdullahi

Bayanan da suke fitowa daga ofishin sakataren Gwamnatin Najeriya na cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Mista Godwin Emefiele, CFR daga aiki ba tare da bata lokaci ba.
Bauanin hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya Willie Bassey ya fitar a yammacin ranar Juma’a.
Daga Imrana Abdullahi
A cewar sanarwar, dakatarwar “ta biyo bayan binciken da ake yi ne a ofishinsa da kuma sauye-sauyen da ake shirin yi a bangaren hada-hadar kudi na tattalin arzikin kasar.
“Sabarwar ta ce an umurci Emefiele da ya gaggauta mika al’amuran ofishinsa ga Mataimakin Gwamna mai kula da Ayyuka,
Mista Folashodun Adebisi Shonubi, wanda zai yi aiki a matsayin Gwamnan Babban Bankin kasar, har sai an kammala bincike da kuma gyara.”