…Har Yanzu Gwamna Dauda Lawal Bai Ci Bashin Ko Kwabo Ba
Daga Imrana Abdullahi
Shugaban riko na jam’iyyar PDP na Jihar Zamfara Alhaji Muktar Lugga ya bayyana Gwamna Dauda Lawal a matsayin mai kokarin ceton Jihar daga cikin yanayin da aka Sanya ta a ciki tsawon shekaru.
Muktar Lugga ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da wakilin mu a garin Kaduna jim kadan bayan kammala taron shiyyar Arewa maso Yamma na jam’iyyar PDP da ya gudana a Kaduna.
” Muna kara yi wa Allah godiya da ya ba mu ikon halartar wannan babban taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP shiyyar Arewa maso Yamma karkashin jagorancin shugaban mu Sanata Bello Hayatu Gwarzo. Kuma mun yi tattaunawa ne a game da batun yi wa yayan jam’iyya rajista da ake yi kafin lokacin zaben shugabannin jam’iyyar da za a yi nan gaba”.
” Duk tattaunawar da aka yi mun gane lallai cewa PDP na nan a wannan yanki kuma ta na a kan kafafunta kuma da yardar Allah irin shirin da muke yi ina yi wa jama’a albishir cewa wannan yankin Arewa maso Yamma duk sai ya koma PDP wannan shi ne tunanin mu, saboda haka taro ya yi kyau shugabanni sun yi jawabi sannan shugabannin jam’iyya guda Bakwai na wannan shiyyar duk sun halarta kowa ya bayar da gudunmawarsa
Hakika duk wani mai babbar riga da yake ganin dan siyasa ne mun tika shi kaye kuma duk lokacin da aka sake kada kugen siyasa a lokacin zabe sai mun tika su kaye da ikon Allah.
” Daman can ashe abin da Jihar Zamfara ke samu zai Isa a yi wa jama’a aiki, illa dai kawai wawurewa ake yi, amma a yanzu muna yi wa Allah godiya da Gwamna Dauda ke kokarin saita al’amura a Jihar Zamfara”.
” Ganin cewa Gwamna Dauda shi ne kadai a wannan shiyyar ta Arewa maso Yamma irin ayyukan ci gaban da yake aiwatarwa ya nuna cewa hakika da gaba daya an ba PDP wannan kasa, to, da yankin an wuce irin wannan tafiyar hawainiyar da ake yi.
” Hakika Gwamna Dauda ya kawo wani abu da yake sabo a cikin al’ummar mu ta Jihar Zamfara da ya bayyana a fili cewa daman irin kudin da ake samu daga Gwamnatin tarayya zai ishe mu aiki ga shi yau rana daya ya tona masu asiri ashe wawure kudin ake yi kawai, sai ga shi ya nuna lallai kudin da ake samu an rabon kasa sun Isa su yi wa jama’a aiki.
Lugga ya ci gaba da bayanin cewa ya na son ya jawo hankalin jama’a cewa har yanzu Gwamna Dauda bai ci bashi ko na naira daya ba duk abin da ake yi ana yi ne daga kudin da Jiha ke samowa daga asusun Gwannatin tarayya, ina ga zuwa nana gaba kadan idan ya kara saita abubuwa ya zamanto kudin shiga na jiha ya karu wannan kawai sakaci ne tun da ga shi Gwannatin tarayya ta kasa abin da Gwamnatin tarayya take yi saboda haka mu kwantar da hankalin mu domin Allah ubangiji ya nuna mana ranar da muke bugun gaba mu ce abin da muka fito muka nema shi ne mulki kuma mun iya shi domin zaben Gwamna Dauda abu ne da aka kafa tarihi da shi kuma duk wani da yake ganin ya na da babbar riga wai shi dan siyasa ne mun tika shi kaye kuma ko gobe suka fito za mu kara tika su kaye ba wani abu ba ne Allah keyi kuma gare shi muka tsaya.