SAKAMAKON kokari da jajircewar da ta Sanya dan takarar neman kujerar majalisar wakilai ta tarayya domin wakiltar kananan hukumomin Zurmi da Shinkafi da ke Jihar Zamfara ya sa Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi Sarkin Shanun Shinkafi na farko ya nada wadannan mutane a matsayin Jagororin yada manufofinsa a Shinkafi da Zurmi da nufin kwalliya ta biya kudin sabulu wato dai haka ta cimma ga ci kowa ya amfana.
Ana saran dai wadannan zaratan mutane da suka saba yada manufofi ta hanyar rubuce rubuce a kafafen Sada zumunta na zamani za su kara matsa kaimin yin aiki domin tallata manufofin Sarkin Shanun Shinkafi na farko, dan Gwagwarmaya Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ta yadda duniya da dukkan masu zabe Maza da mata za su Ankara har a samu gudunmawarsu.
Ita dai wannan kungiyar yada manufofin a dandalin yanar Gizo sunan ta Sarkin Shanu Media Team da aka nada ko- dinetocin tafuyar tun daga Abubakar Lauwali Shinkafi a matsayin kodinetan shiyya da kuma shugabannin mata sai shugabanni a kowace karamar hukuma a kananan hukumomin Shinkafi da Zurmi.
Domin kowa ya san su ya san sunayensu ga sunan.