Allah Ya Kara ma Koshin lafiya, Ya ta-da kafadun Ka, don Kaunar da Allahu Subhana huwa Ta-Allah Ya ke yiwa Annabin Rahama, Annabin Tsira, Cikamakin Annabawa, Muhammadu S.A.W.
Godiya ga dukkanin Al’umar Musulmi da suka je Ziyarar dubiya ga Maigirma Magayakin Hadejia Alhaji Muhammad Ibrahim Umar Nabagara.
Musamman Maimartaba Sarkin Hadejia Alhaji Dr. Adamu Abubakar Maje Haruna Abdul’Kadir, C.O.N. Wanda Maigirma Galadiman Hadejia Alhaji Usman Abdul’Azeez Zakariyya ya Wakilce Shi a Wurin Ziyarar dubiya dangane da rashin lafiyar ta Magayakin SARKI.
Hakanan , godiya ta musamman ga Maigirma Sanatan Kasar Hadejia, Wanda ya kasance Cikin Rukunin Manya Kuma fitattun ‘Yan Siyasa na Kasa, da ya Kai Ziyarar dubiya ga Maigirma Magayakin na Hadejia, Wato, (Early Caller).
Maigirma Magayakin na Hadejia Alhaji Muhammad Ibrahim Umar Nabagara yana kwance ne a Asibitin Kwararru Mai Suna PRIME SPECIALIST HOSPITAL dake Karamar Hukumar Tarauni. Ta na kusa da Rukunin Gidaje na Lamido Crescent da Kuma Suleiman Crescent a Birnin Kano.
Kamfanin Sadarwa na Atafi Communications Abuja, ya rawaito cewa, Maigirma Magayakin na Hadejia, yana Samun Sauki SOSAI, da iKon Allah.
Haruna Aliyu Hadejia Atafi Communications Abuja
GSM::::08037879435
GMAIL:::: harunaaliyuhadejia406@gmail.com
THESHIELD Garkuwa