Daga Imrana Abdullahi
A ƙalla a yau ranar 4 ga watan Afrilu,2026 ne makarantar haddar Al- Kur’ani mai suna Daru Sigaril Huffaz, karkashin jagorancin Shaikh Abdulrahman Usman Zakariyya suka yaye dalibai wadanda suka haddace Alkur’ani mai girma su 37 a garin Kaduna.
An dai yi gagarumin taron ne a dakin yin taro na dandalin tunawa da Murtala da ke cikin garin Kaduna.
A wurin taron saukar karatun Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmad Nuhu Bamalli, ya bukaci daukacin ya’yan Musulmi a fadin Najeriya da su kara matsa kaimi wajen yin haddar Alkur’ani Mai tsarki tare da yin aiki da shi.

Mai Martaba Sarkin ya bayar da wannan shawarar ce a wajen taro karo na hudu da makarantar Daru Sigari Huffaz da ke cikin garin Kaduna ta shirya domin yaye dalibai Maza da Mata da suka haddace Alkur’ani Mai tsarki.
Sarkin wanda Hakimin Gabasawa Wazirin dan Galadima Zazzau Alhaji Shitu ya wakilce shi kuma ya karanta sakonsa a wurin taron inda ya ce Mai Martaba Sarki ya ce lallai a gaya wa yara dalibai da suka yi wannan sauka da cewa su sani wannan ne matakin ilimin farko a gare ku don haka ku sani cewa a yanzu ne fa zaku shiga cikin Kogin ilimi domin kara samun ilimin da ke da fadi sosai.

Shi kuwa a nasa jawabin babban Bako mai gabatar da Kasida shugaban hukumar jindadin Alhazai ta Jihar Kaduna Malam Salihu S Abubakar, jawabi ya yi a kan muhimmancin neman ilimi a cikin addini a tsakanin Musulmai.
Shima Shaikh Abdulrahman Zakariyya Usman ( Hunain), wanda shi ne shugaban makarantar bayani ya yi a kan babban kalubalen da makarantar ke fuskanta na farko shi ne makarantar ba ta da matsuguni na ta, amma ya ce shi mafarkinsa shi ne a samu wurin haddar Alkur’ani mai kyau ingantaccen da idan ana yi wa dalibai karatu idan an zo ana yi masu karatu a kan batun maganar Kifi akwai wurin da za a nuna masu mai kamar wannan haka kuma duk inda aka zo za a ga ga dai misalin da ake nunawa a aikace, kamar yadda abin yake a wadansu kasashen da suka ci gaba.

Sannan kuma Shaikh Abdulrahman ya ci gaba da cewa akwai wani babban kalubalen da ake fuskanta a wannan makaranta wurin yin haddar ma sai kaga dalibai ma kamar kawai a makarantar ne ma suke yin haddar idan an ta fi gida kuma shike nan, amma abin da muke bukata shi ne dalibai su samu sukunin yin karatun cikin natsuwa da walwala domin yin haddar littafin Allah.
Wasu daga cikin iyayen yaran sun bayyana jin dadinsu da irin yadda ƴaƴansu suka samu yin haddar
Muhimman mutane da suka hada da alarammomin Alkur’ani a ciki da wajen jihar Kaduna ne suka halarci wajen taron yaye dalibai 37 da suka haddace Alkur’anin a makarantar Daru Sigaril Huffaz kuma.masu shekaru a ƙalla Goma da haihuwa.

THESHIELD Garkuwa