Daga Imrana Abdullahi
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sakataren Gwamnatin tarayyar Najeriya tsohon Sanata George Akume, ya bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya canza wadansu ministoci guda biyu na Kudi Misra Wake Edun da Ahmed Musa Dangiwa za su bar majalisar zartarwar ƙasar inda kuma tuni aka ambata sunayen wadanda za su maye gurbinsu
Kafin dai zuwa yanzu da lamarin ya faru Mista Edun ne ministan Kudi da tsare tsaren tattalin arziki. Wanda kuma aka ce masa ya mika ragamar tafiyar da ma’aikatar a hannun
Mista Taiwo Oyedele wanda a halin yanzu zai rike ma’aikatar a matsayin ministan Kudi kuma ministan tsare tsaren tattalin arzikin kasa, kuma kafin hakan shi ne ministan kasar a ma’aikatar.
Sai kuma Dokta Muttaqha Rabe Darma shi ne aka bayyana a matsayin wanda aka zaba ya zama minista a ma’aikatar Gidaje da bunkasa birane.
Sanarwar takardar ta kuma umarci Dangiwa ya mika ragamar ma’aikatar a hannun ministan kasa na ma’aikatar.
Sai takardar ta ci gaba da cewa “ana son a kammala mika dukkan ragamar ma’aikatun biyu ga ministocin kasa da za su rike kafin rufe ayyukan ranar Alhamis 23 ga watan Afrilu, 2026.
THESHIELD Garkuwa