Home / Labarai / Shugaban PDP Na Kasa Ya Mika Ta’aziyyarsa Ga Gwamna Tambuwal

Shugaban PDP Na Kasa Ya Mika Ta’aziyyarsa Ga Gwamna Tambuwal

Daga Imrana Abdullahi

….Bisa Rasuwar Mai Ba Gwamna Aminu Waziri Tambiwal Shawara

Dokta Iyorchia Ayu, shugaban jam’iyyar PDP na kasa ya mika sakon ta’aziyyarsa ga Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal bisa rasuwar Hajiya Aisha Maina,mai bayar da shawara ta musamman a kan harkokin ilimin yaya mata

Ayu ya bayyana hakan ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Yusuf Dingyadi mai taimaka masa a kan harkokin yada labarai inda ya bayyana rasuwar a matsayin wani babban rashi ga Jihar Sakkwato,PDP da kasa baki daya.

Ya ce marigayiyar ta yi rayuwar abar koyi , saboda hakuri da aiki tukuru da ta yi aiki domin ci gaban yara da daukacin dukkan iyali baki daya, Wanda hakan yasa ta bar wani gurbi mai wuyar cikawa.

“Ta kasance daya daga cikin mata kalilan a cikin Jihar da ta bayar da gudunmawarta wajen gina kasa inda masu karamin karfi za su amfana a samu ingantaccen zaman lafiya da kwanciyar hankali da ta dade ta na kokarin mata sun samu Hakkinsu da ya dace su samu a kowane matakin Gwamnati”.

Hakika wannan rashin lamari ne da ke Sosa rai tun daga Jihar Sakkwato da kasa baki daya”, Inji Ayu.

Shugaban jam’iyyar na kasa ya kuma yi addu’ar Allah ya ya gafarta wa marigayiyar

Ya kuma jajantawa da iyalansa baki daya
Gwamnan na Sakkwato da iyalansa baki daya game da wannan rashin
In dai zaku iya tunawa Maina ta rasu ne a asibitin koyarwa na jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato jim kadan bayan ta halarci babban taron PDP na dan takarar shugaban kasa a Jihar a ranar Talata.

About andiya

Check Also

Edo 2024: Group Hold Symposium In Support Of Asue Ighodalo

  The Good Governance Advocacy Group, has held a symposium to drum their support for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.