Daga Imrana Abdullahi
Wadansu ina da kisa da ake kyautata zaton cewa ‘yan ta’adda ne sun kai wani mummunan sabon hari kan manoma a wasu ƙauyukan Jambako, Sakida da Saulawa na Ƙaramar Hukumar Maradun da ke Jihar Zamfara kuma sun kashe mutum 25.
Kamar yadda rahotannin suka tabbatar Wani ganau ya ce, ‘yan bindigar sun kai hari kan mutanen ƙauyen ne a lokacin da suke aiki a Gonakinsu da safiyar Asabar.
Wani mazaunin ƙauyen Sakida mai suna Malam Ɗayyabu ya shaida wa wakilinmu ta wayar cewa, an kashe mutum 21 a Jambako, sannan biyar daga Sakida da Saulawa sun samu raunuka.
A cewarsa, ‘yan bindigar sun fara kai wa mutanen Sakidda hari ne a Gonakinsu, inda wasu ‘yan ƙungiyar ’yan banga daga Jambako suka garzaya don yaƙar su, inda aka rasa mutum 18 sakamakon musayar wutar da aka yi tsakanin ɓangarorin biyu.
“Kamar yadda nake magana da ku yanzu, mun binne mutum 21 a garin Jambako da rana, yayin da sauran biyar din ‘yan ƙauyen Sakida aka binne da yamma kamar yadda addinin Musulunci ya tanada,” in ji Malam Dayyabu.
Da aka tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar, cewa ya yi alƙawarin zai yi tsokaci nan gaba.