Home / News / Majalisar Dattawa Ta 10: APC Ta Zabi Manyan Shugabannin Ta

Majalisar Dattawa Ta 10: APC Ta Zabi Manyan Shugabannin Ta

 

Kamar dai yadda jaridar the Nation ta ruwaito cewa APC Jam’iyyar  mai mulki ta zabi manyan jami’an majalisar dattawa ta 10.

In dai zaku tuna cewa Godswill Akpabio, da Jibrin Barau, an zabe su ne a ranar 13 ga Yuni, 2023 a matsayin shugaban majalisar dattawa da mataimakin shugaban majalisar ya kasa, domin su tafiyar da jagoranci da kuma ayyukan majalisar.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, jam’iyyar ta zabi Sanata Opeyemi Bamidele daga jihar Ekiti a matsayin shugaban masu rinjaye na  majalisar dattawa, sai kuma Sanata Dave Umahi daga jihar Ebonyi a matsayin mataimakin shugaban masu rinjaye na  majalisar.

Sai kuma Sanata Ali Ndume daga jihar Borno ya zama babban mai tsawatarwa,yayin da Sanata Lola Ashiru daga jihar Kwara ya zama mataimakiyarsa.

Jam’iyyun adawa karkashin jam’iyyar PDP na ci gaba da fafutukar ganin sun tsayar da ‘yan takarar shugaban marasa rinjaye.

cewa yayin da tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal ke kan gaba a matsayin wanda aka fi so a wannan mukami, sauran da ke fafutukar ganin sun hada da Sanata Abdul Ningi, da ake ganin yana da goyon bayan Nyesom Wike, da Sanata Jarigbe Jarigbe duk na cikin yan takarar shugaban marasa rinjaye.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.