Home / Labarai / Gwamnan Neja Ya Amince Da Rusa Hukumomi, Ma’aikatun Gwamnati A Jihar

Gwamnan Neja Ya Amince Da Rusa Hukumomi, Ma’aikatun Gwamnati A Jihar

Daga Imrana Abdullahi

Gwamnan jihar Neja, Umar Bago ya amince da Rusa wasu hukumomi da Ma’aikatun Gwamnatin Jihar.

Sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar  Abubakar Usman ya fitar a ranar Litinin, ta kuma sanar da soke duk wasu nade-naden siyasa da aka yi kafin ranar 29 ga Mayu, 2023.

A cewar sanarwar, rushewar  ta hada da na ka’ida da na hukumar da ba na doka ba

A yayin da Sakataren Gwamnatin ya yaba  da irin gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban jihar da kuma harkokin ofishinsu.

Sanarwar ta kuma umarci hukumomin da abin ya shafa da su mika dukkan kadarorin gwamnati da suka hada da motocin hukuma da ke hannunsu ga babban Daraktan da ke hukumar da suke aiki .

About andiya

Check Also

Abdullahi Tumburkai Wins PDP Primary Election, Secures Nomination for Katsina Council Election

Abdullahi Usman Tumburkai has on Wednesday 15/05/2024 triumphed in the Peoples Democratic Party (PDP) primary …

Leave a Reply

Your email address will not be published.