….da kiraye-kirayen shiga tsakani daga waje
Daga Imrana Abdullahi
Kungiyar kawancen Najeriya da Nijar a ranar Juma’a ta yi Allah wadai da juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Nijar tare da yin kira da a tsoma bakin kungiyoyin kwadago a Afirka.
Malam Ahmad Altine, shugaban kungiyar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja.
Ya ce: “Kungiyarmu ta yi Allah wadai da juyin mulkin da aka yi a jamhuriyar Nijar.
“Muna kira ga Kungiyar Tarayyar Afirka da Kungiyar Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) da kuma Majalisar Dinkin Duniya da su matsa lamba kan gwamnatin mulkin sojan da ta gaggauta maido da mulkin dimokradiyya a Jamhuriyar Nijar.”
Shugaban ya ce kungiyar ta jajantawa iyalan Shugaban kasa Muhammad Bazoum saboda irin halin da suke ciki a halin yanzu.
Altine ya yi kira ga dukkanin kungiyoyin fararen hula a Jamhuriyar Nijar da su yi tir da juyin mulkin.