Related Articles
Daga Imrana Abdullahi
Injiniya Dokta Aliyu Muammd Waziri Santurakin Tudun wada Kaduna kuma shugabn kungiyar noman zamani na kasa da ke dauke da mambobi miliyan 25 ya yi kira ga Gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin Asiwaju Bola Ahmad Tinubu da ta nemo ainihin kudin da Gwamnatin Buhari ta bayar domin ci gaban harkokin Noma.
Aliyu Muhammad Waziri dan marayan Zaki ya yi wannan kiran ne jim kadan bayan karbar lambar karramawa daga kungiyar Mawallafa jaridu ta Arewacin Najeriya.
Kungiyar Mawallafa ta dai dauki matakin Karrama Dokta Aliyu Muhammad Waziri ne bisa la’akari da kwazon taimakawa kasa da yake yi ta fuskar bunkasar tattalin arziki da kuma bunkasa harkokin Noma da Kiwo.
Ya kuma bayyana cikakken farin cikinsa da abin da kungiyar Mawallafa jaridu da mujallu ta arewacin Najeriya suka yi masa da a cikin dubu suka zakulo shi sannan aka karramashi da lambar yabawa.
“Hakika ba zan mance da wannan kokarin karramawar da aka yi masa ba don haka ina godiya, murna da farin ciki kwarai”.
” a matsayina na mai kokarin samawa matasa abin yi hanyar Noma zamani kowa ne matashi ya zama mai dogaro da kansa”.
Aliyu Waziri ya ci gaba da cewa ya na kokari ne domin ganin matasa da sauran yan Najeriya sun ci moriyar irin yadda ake yin Noma irin na zamani ta hanyar yin amfani da na’u’rorin zamani ba kamar yadda ake yi ba a can baya ta hanyar yin amfani da aiki da hannu”.
Ya kara da cewa ta hanyar yin amfani da kwakwalwar da Allah ya bashi ne ya nemi tsohuwar Gwamnatin Buhari ta taimakawa da manoman zamani ta yadda za a Kori yunwa da talauci a kasa.
“Idan abin ya tabbata kowace shekara zamu dauki matasan da duka yi karatu suke bautar kasa a kalla dubu biyu a kowace shekara a Koyar da su sana’ar da za su dogara da kansu. Haka kuma jami’an tsaro da yan jarida duk za su samu yin Noman nan ba tare da samun takara ba kuma suma mata da ke a cikin gidaje za a Koyar da su Noman Kaji ba tare da sun fita waje suna yawace yawace ba wanda hakan zai taimakawa magidanci mai karamin karfi matsalar daukar larurar gidansa. Kuma za a rika yin harkar saye da sayar da kayan amfani Gona ta hanyar yin amfani da hanyar cinikayya ta hanyar amfani da yanar Gizo”.
Saboda haka ne muka godewa tsohuwar Gwamnati karkashin Muhammadu Buhari da ta ba mu dama da zarafi yin abin da muka yi.
“Hakan ya sa suka je kasashen waje cikin kasashe guda uku aka samo bashin dalar Amurka miliyan dubu 1 da miliyan dari daya duk da nufin inganta Noman zamani, kasashen da suka bayar da wannan kudi su ne Brazil, Jamus da Swizerland kuma an samo kudin ne a shekara ta 2019, wanda a karkashin jagorancin da nake yi na kungiyar Noman Zamani mun samu zama da shugaba Buhari da kuma marigayi Abba Kyari shugaban ma’aikatan gidan Gwamnati da muka tsara abubuwan baki daya haka dai aka amso kudin aka kuma shigo da su cikin Najeriya aka ajiye kudin har ita ma Gwamnatin Buhari da kara dala miliyan dari a kai da Gwamnati da mukarrabanta duk sun amince a bayar da bashin a raba wa manoma musamman wadanda suke a kauye wato karkara da suke Noma ta yaddanza su sharbi romon Dimokuradiyya, duk fa bayan kudade da yawa da aka bayar ne”.
“Amma duk da wannan kokarin na Gwamnati sai ga masu manyan riguna da ake kira Malum- malum karkashin jagorancin wadansu mutane daban daban da suka hada har da malaman addini da idan mutum ya saba rigar sai ya yi sama da taraktoci masu dimbin yawa. Domin an samu wani tsohon ministan da ya yi haka ya yi kwana da manyan kaya na taraktoci da yawa
A bisa hakan mun yi Allah wadai da tsofaffin ministoci da suka yi Barna har suka Sanya shugaban kasa a Kunya.Saboda mu har gobe muna tare da irin kudiri tsohon shugaba kasa Buhari domin ba maciyin Amana ba ne sabanin sauran wadanda suka yi ministoci a karkashinsa da suka yi kokarin sai an Jefa kasar cikin wahala a ci zarafin yan kasa, ga kuma hana yin kasuwanci da walwala da suka wawushe kudin da sunan bayar da rancen Ankoborowa da aka rika rubuta takarda kawai ana Karbe kudin wanda har ya kai ga wadanda suka karbi kudin kasa da Digo biyu zuwa uku ne kawai ya kai hannun manoman wanda kashi Casa’in da Tara da Digo Takwas duk sun ta fi ne a hannun masu manya manyan riga kuma kudin na girinsu sun yi mursisi.
Hakika ” muna goyon bayan a kafa kwamitin kwato wadannan kudin da duk wata kungiyar da ta shafi ta Noma da wadanda suka kira kansu da sunan Noma har shi tsohon ministan da irin mu na can kasa kungiyoyin Noma da aka ce sun karbi bashin kudin daga Babban Bankin Najeriya da kuma Bankunan yan kasuwa tun daga irinsu har irin mu duk a ce kowa ya dawo da kudin. Kudi na Najeriya ne kuma masu son yin Noma.
Aliyu Waziri ya ce an wayi gari an yi ministan Gona dan Jihar Kaduna da ake ganin za a samu ci gaban Noma ta yadda za a raya mutanen karkara a samu amfani mai yawa da kuma fitar da shi kasashen waje daga Najeriya. Amma sai gashi an wayi gari duk shekara ana fitar da kasafin kudi domin Noma amma ba wani labari, kai wace jiha ce aka kai taraktar Noma? shin an kai tarakta ko irin shukawa?
A matsayina na shugaban kungiyar manoman Najeriya da ke magana da yawun mutane miliyan 25 ya dace in yi kira ga yan jarida da su tambayi me aka yi da kasafin kudin da aka yi a kan harkar Noma? don haka alhaki na ga yan Najeriya da suka hada da jami’an tsaro a lalubo abin da aka yi da wadannan kudin a can baya. Wanda bayan gano kudin za a Sanya su a inda yakamata.
“Wannan kungiya ta wa ta masu Noman zamani a waccan Gwamnatin na nemi a mayar da shi wata hukumar bayar da taimakon yin Noma kuma wannan kungiyar ta wa ( national Agricultural Mechanization co-operative of Nigeria) amma na roki shugaban kasa Buhari ya mayar da ita National Agricultural Mechanization development Fund kuma ya yi alkawarin zai ba mu kudin da za a yi aikin fadada harkar Noma da samar da abinci da kasuwancin saye da Sayarwa na kayan amfanin Gona da ake samu daga Najeriya ta yadda za a babbako da tattalin arzikin kasa domin idan kasa ba ta da yadda za ta samar da kaya a kasar ta hakika akwai ci baya a kowace kasa ce.
Misali kamar mutum ne ya zauna baya iya yin neman kudi “Sai dai kawai a kullum ka Zara ka kashe ba fita a nemo ai za a iya wayar gari mutum ba shi da ko Kwabo to kamar haka ne, hakan ta Sanya muke yin addu’ar Allah ya taimaki shugaba Muhammadu Buhari ya sa ya gama lafiya cikin Aminci, su kuma wadanda suka ci Amanar mu a kullum muna yin kira ga jami’an tsaro da a bisu a dawo mana da kudin mu, hakan ta Sanya muke yin kira ga kafafen yada labarai su tambayi inda aka kai taraktocin Noma a ma’aikatar Gona a can baya indai ba a yau za a yi ruwanta a kawo ta ba wanda lokaci ya kure, Allah ya tsare.