Home / Labarai / Gwamna Dauda Lawal Ya Fara Biyan Mafi Karancin Albashi Na Dubu 30 A Lokaci Guda

Gwamna Dauda Lawal Ya Fara Biyan Mafi Karancin Albashi Na Dubu 30 A Lokaci Guda

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya fara biyan mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 30 ga ma’aikatan Jihar, a lokaci guda kuma har ya biya albashin watan nan na Yuni saboda shagalin babbar sallah.
A watan da ya gabata ne gwamnan ya bayyana a wata ganawa da ya yi da shugabannin Ƙungiyar Ƙwadago ta Jihar Zamfara cewa zai fara biyan mafi ƙarancin albashi a watan Yuni.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Gusau, mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa ma’aikatan jihar Zamfara sun fara karɓar albashin su ne a ranar 12 ga watan Yuni, gabanin bikin Babbar Sallah.
Ya ƙara da cewa, gwamnatin jihar ta cika alƙawarin da ta ɗauka na biyan ma’aikata mafi ƙarancin albashi, wanda hakan ya nuna ƙarara a cikin albashin watan Yuni da ta riga ta biya.
“Gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal, ta biya albashin watan Yuni domin tallafa wa ma’aikata a shirye-shiryen gudanar da bukukuwan Babbar Sallah.
“Wannan ya yi daidai da cika alƙawarin da gwamnan ya yi a watan jiya na aiwatar da mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 30.
“Kafin yanzu, ma’aikatan gwamnati a Zamfara na karɓar mafi ƙarancin albashin  Naira dubu bakwai ne kacal.
“Gwamnatin Dauda Lawal ta kasance mai son ma’aikata tun lokacin da aka kafa ta, inda ta tabbatar da biyan albashin watanni uku da aka hana su, kuɗaɗen hutu, basussuka, da biyan albashi a kan kari.
“Gwamnati za ta ci gaba da ƙoƙarin kawo gyara da kuma farfaɗo da ma’aikatan jihar Zamfara,” in ji sanarwar.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.