Home / Uncategorized / GWAMNA LAWAL YA BA DA TABBACIN KARIYA DA TSARO GA ‘YAN YI WA ƘASA HIDIMA (NYSC) A ZAMFARA

GWAMNA LAWAL YA BA DA TABBACIN KARIYA DA TSARO GA ‘YAN YI WA ƘASA HIDIMA (NYSC) A ZAMFARA

 

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yi wa masu hidimta wa ƙasa (NYSC) alƙawarin cewa gwamnatinsa ta duƙufa wajen tabbatar da tsaron lafiyarsu, tare da ba su kariya a duk faɗin jihar.

Gwamnan ya ƙaddamar da bikin buɗe rukunin Batch ‘C,’ Stream 2 na ‘yan yi wa ƙasa hidima NYSC na 2024 a ranar Juma’a, wanda ya gudana a sansanin wucin-gadi da ke harabar Hukumar UBEC da ke Gusau.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya ce an dawo da sansanin horar da masu yi wa ƙasa hidima na NYSC a Zamfara ne a watannin da suka gabata, inda aka ɗora daga rukunin Batch ‘C,’ stream 1 na 2024.

Sanarwar ta ƙara da cewa, an dawo da ayyukan sansanin a Zamfara ne sakamakon dawowar zaman lafiya da kuma raguwar ayyukan ’yan bindiga a faɗin jihar.

Gwamna Lawal ya zagaya faretin girmamawa na ’yan NYSC kafin ya bayyana buɗe sansanin.

A nasa jawabin, gwamnan ya ce shirin na NYSC ya inganta haɗin kan ƙasa matuƙa tare da samar wa al’ummomi daban-daban ƙwararrun ma’aikata masu inganci.

“Mu a jihar Zamfara mun shaidi tasirin ayyukan da ƙwararrun ’yan NYSC ke yi a duk sassan tattalin arziki. Suna ba da gudunmawa ba tare da son kai ba ga muhimman fannoni kamar ilimi, lafiya, da noma.

“Haƙiƙa shirin ya ƙara wa ƙoƙarin gwamnati izza wajen biyan buƙatun al’umma. Don haka sake dawo da ayyukan NYSC a Jihar Zamfara, ya zama wani gagarumin ci gaba a wannan tafiya tamu ta maido da kwarin gwiwa da kwanciyar hankali da ake buƙata a jihar.

“Mun yaba da gudunmawar ku kuma muna ba ku tabbacin goyon bayan gwamnati kan manufofin shirin. Za mu ba da tallafi don taimaka muku don mayar da jihar Zamfara sabon gidan ku.

“A matsayinku na matasa masu ilimi, kuna da alhakin bayar da gudunmawa wajen tsara makomar wannan al’umma. Ku ne abin koyi ga miliyoyin matasa a duk faɗin ƙasar waɗanda halayenku zai zama abin koyi.

“Ina tabbatar muku da ƙudurinmu na tabbatar da jin daɗin ku, kariya, da tsaro a duk inda za a tura ku don ayyuka na farko.

“An san mutanenmu yawan karimci wajen karbar baƙi da son zaman lafiya. Ku yi cuɗanya da su cikin mutunci da girmama al’adunsu da addininsu don samun amincewarsu. Ina da yaƙinin za ku samu jituwa da al’ummomin da aka tura ku ku yi wa hidima.

“Ina kira gare ku da ku binciki ɗimbin damammaki a jihar yayin zaman ku. Ina fata cewa bayan shekarar hidimarku, za ku yi amfani da wasu damar, kamar na noma.

Gwamnan ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa ta samu gagarumar nasara wajen ginawa da inganta ababen more rayuwa cikin watanni 20 da suka gabata.

“Ayyana dokar ta-baci kan ilimi da lafiya ya baiwa jihar damar mai da hankali sosai kan sauran bangarori masu muhimmanci.

“Yanzu mun buɗe sabon babi a Jihar Zamfara, tare da cika alƙawari ga ɗimbin al’ummar jihar, ciki har da jama’ar sauran sassan ƙasar nan masu son shiga wannan tafiya.

“A madadin ɗaukacin nagartattun al’ummar jihar Zamfara, ina yi muku maraba da zuwa jiharmu mai albarka, gidan noma da ma’adanai. Ina kira gare ku da ku ɗauki wannan horo da muhimmanci kuma ku halarci duk karatuttukan da za a gudanar da sansani. Da wannan, nake farin cikin ayyana ƙaddamar buɗe rukunin NYSC 2024 na Batch ‘C,’ Stream 2. Ina yi muku fatan alheri da kuma shekarar hidima mai albarka.”

Tun da farko, Kodinetan NYSC na jihar Zamfara, Mallam Muhammed Lawan Ahmed, ya yaba wa Gwamna Lawal bisa goyon bayan da gwamnatinsa ke bayarwa wajen ganin an samu nasarar shirin.

About andiya

Check Also

GWAMNA LAWAL YA YABA WA HUKUMAR TSARO TA DSS KAN KAMA MAKAMAI A ZAMFARA, YA CE ‘YAN TA’ADDA NA CIKIN TASKU

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya yaba wa Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) …

Leave a Reply

Your email address will not be published.