Home / Uncategorized / Gobe Talata Obasanjo Zai Ƙaddamar Da Asibitin Yariman Bakura, Tare Da Wasu Ayyuka A Zamfara

Gobe Talata Obasanjo Zai Ƙaddamar Da Asibitin Yariman Bakura, Tare Da Wasu Ayyuka A Zamfara

 

Tsohon shugaban ƙasar nan, Chief Olusegun Obasanjo zai shiga jihar Zamfara domin ƙaddamar da wasu ayyukan da Gwamna Dauda Lawal ya yi a jihar, wanda zai haɗa da babban asibitin Yariman Bakura da kuma wasu hanyoyi a babban birnin jihar.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar a Gusau yau ɗin nan, ya bayyana cewa a gobe Talara 17 ga wannan wata na Yunin 2015 ne Tsohon shugaban ƙasar zai gudanar da waɗannan ayyuka.

Sulaiman Bala ya ƙara da cewa wannan asibiti da Obasanjo zai buɗe, asibiti ne da aka yi wa ingantaccen gyara, tare da wadata shi da kayan aiki irin na zamani.

“Haka kuma, Tsohon shugaban ƙasa Obasanjo zai ƙaddamar da wasu tituna a Unguwar GRA ta Guasau, wacce ta kasance ɗaya daga cikin ayyukan da gwamnan ya aiwatar a shirin gwamnatin sa na sake inganta biranen jihar,” in ji sanarwar.

About andiya

Check Also

10,000 South East Pupils Get School Bags From Collins Onyeaji Foundation

    No fewer than 10,000 pupils in the South East Zone of Nigeria are …

Leave a Reply

Your email address will not be published.