Home / Big News / Zamfara Ta Tashi Daga Matsayi Na 36 Zuwa Na 17 A Shekara Biyu Ƙarƙashin Gwamna Lawal — Rahoton BudgIT

Zamfara Ta Tashi Daga Matsayi Na 36 Zuwa Na 17 A Shekara Biyu Ƙarƙashin Gwamna Lawal — Rahoton BudgIT

 

Daga Imrana Abdullahi

Jihar Zamfara ta samu babban ci gaba a fannin gudanar da harkokin kuɗi, inda rahoton BudgIT ya nuna cewa jihar ta haura daga matsayi na 36 a 2023 zuwa matsayi na 17 a 2025, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal.

Wannan sabon rahoto na 2025 State of States ya nuna cewa Zamfara ta ƙarfafa kasafin kuɗinta fiye da yadda ake gani a wasu jihohi, tare da rage dogaro da kason kuɗin Gwamnatin Tarayya.

A cewar BudgIT, jihar ta tashi daga matsayi na 26 a 2024 zuwa 17 a bana, alamar tsari da sauye–sauyen kuɗaɗe da aka gudanar cikin tsari.

A shekarar 2023 lokacin da Gwamna Lawal ya hau mulki, Zamfara ta kasance a ƙasan jadawalin a matsayi na 36.

Rahoton ya nuna cewa kuɗaɗen shiga na jihar sun ƙaru da kashi 182.34%, daga naira biliyan 87.44 a 2023 zuwa naira biliyan 246.88 a 2024. Haka kuma jimillar kuɗaɗen shiga gaba ɗaya ta ƙaru zuwa naira biliyan 315.53, ƙaruwar kusan kashi 118%. Haraji da jihar ta tara ya kai kusan kashi 10.31% na jimillar kuɗaɗen shiga a 2024.

BudgIT ta bayyana cewa wannan ci gaban yana nuna Zamfara ta fara rage dogaro ga kuɗin kason asusun tarayya, kuma idan za a yi hasashe, jihar na da ƙarfin kai da kai idan za a kalle ta a matsayin ikon tattalin arziki mai zaman kansa.

A bangaren haraji, jihar ta samu naira biliyan 25.46 a 2024, ƙaruwa ce ta kusan kashi 15% daga naira biliyan 22.16 a shekarar da ta gabata. Har ila yau, kuɗaɗen FAAC sun ƙaru da sama da kashi 239%, daga naira biliyan 65.28 a 2023 zuwa biliyan 221.42 a 2024.

Rahoton ya kuma yi hasashe kan habakar kuɗaxen shiga marasa haraji, inda aka samu ƙaruwa sosai a bangaren lasisi, kuɗin biyan takardu da wasu hanyoyin samun kuɗaɗe. Misali, kuɗaɗen lasisi sun tashi da fiye da kashi 5,900% a shekarar 2023.

A ɓangaren kashe kuɗi, musammam a fannin lafiya da ilimi, rahoton ya nuna ƙarin kuɗaɗen da gwamnati ta zuba, duk da cewa akwai ƙalubalen ingantacciyar aiwatarwa. Jimillar kashe kuɗin lafiya ta tashi daga naira biliyan 4.29 a 2022 zuwa biliyan 11.88 a 2024, inda kashe kuɗi kan mutum ɗaya ya ninka fiye da biyu.

About andiya

Check Also

Gwamna Lawal Ya Gabatar da Kasafin Naira Biliyan 861 Ga Majalisar Dokokin Jihar Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gabatar da ƙudirin kasafin kuɗi na shekarar 2026 …

Leave a Reply

Your email address will not be published.