Home / Big News / Ina Nan Kan Takarata – Shettima Usman Yerima

Ina Nan Kan Takarata – Shettima Usman Yerima

 

Dan takarar neman kujerar dan majalisar dattawa daga yankin mazabar Kaduna ta tsakiya Kwamared Yerima Usman Shettima, ya bayyana cewa ya na Nan a kan matsayinsa na dan takarar majalisar dattawa ba gudu ba ja da baya.
Shettima Usman Yerima ya bayyana hakan ne a wajen wani babban taron manema labaran da ya kira a ofishinsa da ke Kaduna.
Yerima, ya ci gaba da cewa shi a matsayinsa na dan takara karkashin jam’iyyar APC babu wanda ya tuntube shi a game da wata maganar wai an tsayar da wani dan takarar kujerar majalisar dattawa daga yankin Kaduna ta tsakiya, don haka ina don shaidawa jama’a cewa ina Nan a kan matsayin dan takara ba ko wani kokwanto ko na minti ɗaya, takara kawai.
” Kamar yadda kowa ya sani duk inda za a yi wani batun yin Sasanci a harkar siyasa lallai sai an yi zama da dukkan bangarorin da abin ya shafa, sannan kamar Ni a matsayin dan takara zan je in zauna tare da mutane na mu tattauna, amma babu inda hakan ya faru don haka ina nan zan sayi fom din tsayawa takara a kuma shiga filin zabe a fafata idan Allah ya ba mu nasara a ci gaba da fafutukar samun nasarar babban zabe.
“A matsayinsa na dan takarar da ke a kan gaba a yankin Kaduna ta tsakiya ta yaya za a ce irin hakan za ta faru ba tare da wata tattaunawa a tsakanin mu ba yan takara”.
Kamar yadda Shettima Yerima yake fadin cewa ya na yin wannan takara ne domin jama’a ba wai domin kansa kawai ba a matsayinsa na dan gwagwarmayar kwato yancin jama’a da ya dade ana fafatawa da shi tun dadewa.
” Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Sanata Uba Sani ai duk tun muna kananan yan Gwagwarmaya muna tare da su baki daya mun dade muna fafatawa domin kwato yancin jama’a.
Daga ɓangaren Dama Isia Benjamin kenan mai yi wa Kwamared Shettima Yerima hidima a kan batun harkar yada labarai a lokacin gagarumin taron manema labaran
“Ina son fadakar da jama’a cewa lallai ya dace su san cewa ina Nan a cikin takara kuma ba a yi wata magana da Ni ba kai ko ma wata magana mai kama da hakan ba a yi da Ni ba”.
“Don haka a tsarin dimokuraɗiyyar babu batun a je wani wuri a tsara sunan masu takara haka kawai, saboda haka muke shaidawa jama’a cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ma Dan fafutukar tabbatar da dimokuraɗiyyar ne don haka ina saran ba zai amince da wani batun an tsayar da wane ko wane ba tare da an bi tsarin tanadin dimokuradiyyar ba.
Kuma a game da ” batun magoya baya na ina gaya masu cewa ina jiran a fitar da sayar da fom ne domin yan takara su saya Sannan kuma ina jiran ranar da za a je filin zaben fitar da dan takarar da zai tsayawa jam’iyyar APC matsayin dan takarar majalisar dattawa a yankin Kaduna ta tsakiya”.
“Za mu iya kawo shugaban kasa Gwamna da kuma kan mu, wato kujerar majalisar dattawa baki daya a jihar Kaduna, kasancewar mu na wadanda muka yi fafutukar neman jama’a kuma har yau muna tare da jama’a a ko’ina”.
Dan takarar kujerar majalisar dattawa kenan Kwamared Shettima Yerima a lokacin da ya iso wurin taron manema labarai da ya kira a Kaduna.
Halin da muke ciki a yanzu ya sha bamban da abin da muka baro a can baya kuma idan an lura shugaba Bola Tinubu da Gwamna Uba Sani dukkan su yan Gwagwarmaya ne don haka sun san abin da ya dace a tsarin dimokuraɗiyyar
Idan da an tabbatar wa da wadansu mutane da sun san lallai ba su da wani ko wata damar shiga cikin shiga harkar siyasa, domin ba za su iya zuwa wurin jama’a su nemi al’umma domin neman goyon baya.
“Ba wanda ya fi Ni zama ɗan Nigeriya, kuma Ni dan APC be ba wanda zai jefar da Ni a waje daya”, inji Yerima Shettima.
“Mu ba mu jin tsoron Yan adawa, a cikin APC kaaai abin da muke so shi ne mu tabbatar da sanya gidan mu wuri ɗaya ayi tafiya tare”.
Ina kuma yin kira ga jama’a masoya da magoya baya na cewa kada su amince da duk wani bayanin da suke ji ko gani a wani wuri da ba daga wurin ku suka fito ba.

About andiya

Check Also

Dangote, Pope Leo XIV, Trump, Xi Jinping, others Named in TIME 100 Most Influential People for 2026

  Renowned African industrialist and philanthropist, Aliko Dangote, has been named among TIME Magazine’s 100 …

Leave a Reply

Your email address will not be published.