…Na biya mata Umara
Daga Imrana Abdullahi
Wani daga cikin iyayen yaran da suka haddace Alkur’ani mai tsarki a makarantar Daru Sigaril HUFFAZ ya bayyana irin farin cikin da yake tare da shi kasancewar yarsa na daga cikin dalibai 37 mai suna Amina Rabi’u Kakaki.
Alhaji Rabi’u Kakaki ya bayyana cewa a yau ranar kwasar adashi ce kuma muna yi wa Allah godiya da ya ba mu ikon ganin wannan rana da Amina ta haddace Alkur’ani da na dade ina sauraren ganin wannan ranar.
Rabi’u Kakaki, ya ce daman sai da ya je kasa mai tsarki wurin dakin Allah na roke shi a kan ya ba yata damar ta haddace Alkur’ani kuma ga shi Allah ya karbi addu’a ta a yau lamarin ya faru, mun ga wannan ranar, hakika muna yi wa Allah godiya kwarai.
Sakamakon hakan ma Alhaji Rabi’u Kakaki ya kuma biyawa yar tasa kujerar Umara domin ta yi aikin Umara.
Alhaji Rabi’u Kakaki ya na da kukan dadi a wajen wannan taron yaye daliban da suka haddace Kur’ani ya na yi wa Allah godiya.

THESHIELD Garkuwa