Daga Imrana Abdullahi
Dan takarar kujerar majalisar dokoki ta Jihar Kaduna domin wakiltar al’ummar mazabar Doka/Gabasawa da ke cikin karamar hukumar Kaduna ta Arewa Tahir Gambo Abubakar,ya bayyana cewa ya na yin wannan takara ne domin bin umarnin jama’a da suka nemi lallai sai ya tsaya neman wannan kujerar majalisa.
Tahir Gambo ya ci gaba da cewa wannan yunkurin ana yin sa ne domin nemawa jama’a mafita a cikin harkokin rayuwarsu a fannoni daban daban.
Tahir Gambo Abubakar, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Kaduna.
” Mun fito ne domin ni da jama’a ta ne don ba ni kadai ba, tun dadewa ake ta maganar cewa ya dace mu rika zuwa muna bayar da ta mu gudunmawar a siyasance amma ba mu kauracewa siyasa ba ko mun gujewa siyasa ba don haka sai a wannan mataki ne a wannan lokacin ne muka amsa Kiraye – Kirayen da ake yi kama da nufin mu wakilci mutanen karamar hukumar Doka Gabasawa a cikin karamar hukumar Kaduna ta Arewa”.
“Kwarai kuwa jama’ar wannan mazabar dan majalisa ta Doka Gabasawa ne suka nemi sai lallai na tsaya takarar Kujerar dan majalisar Doka/ Gabasawa, saboda a wannan Unguwar Shaba da aka haifi iyaye da Kakanninmu a koda yaushe zaka ga suna yunkurin shiga a dama da su, hakan ya sa wadansu suka ce tun da dai Allah ya sa kai Malam kana hidima da su kana harkoki da su, me zai hana ka shigo domin a fadada wannan kokarin sai ka samu ka shiga cikin siyasa, to, abu dai na Allah ne a lokacin ne na ce masu mu rika yin addu’a dai don har na ce masu A’a,har sai da Allah ya kawo mu wannan lokacin da suka ce don Allah ya dace muzo mu zauna mu fahimci juna saboda muga me za a taimakawa jama’a baki daya a wannan mazabar ta Doka/ Gabasawa”.
A game da batun manufofinsa kuwa, sai Tahir ya kada baki ya ce a koda yaushe muna rokon Allah Ubangiji da ya rika mana idan kuma ya kai mu wannan waje Allah ya ci gaba da tallafa mana, magana ta gaskiya an gaya mana cewa mu rika yi wa magabatan mu biyayya domin tarbiyyar da aka yi mana kenan, abin da ya sa na fadi hakan shi ne domin duk dan majalisa kamar Dan sako ne an aike shi ne domin ya wakilci mutanensa ya muka wa majalisa da sakon jama’arsa da nufin sakon ya isa zuwa bangaren zartarwa na Gwamnati, tun da muna zama da jama’a kuma muna jin kukansu jama’ar da muke cikinsu, akwai wadansu wakilan wadansu kananan hukumomi da ke kokarin ganin jama’ar su sun samu abin da ya dace su samu koda ba dari bisa dari ba, misali a nan karamar hukumar Kaduna ta Arewa akwai wadansu damarmakin da ake da su da kuma za a ce sai wanda yake da karatu ko ilimi mai mataki na kaza ko kaza da za a iya cewa za a ba su matsayin darakta kaza ko na Kaza ko sakataren wata hukuma ta Gwamnati saboda Allah sai kaga daga wannan bangaren na mu sai a rasa irin wadannan mutanen, don haka idan Allah mai kowa mai komi ya kai mu majalisa lafiya a matsayina na dan majalisa lallai zan je da kaina in tabbatar an kai irin wadannan manyan takardu masu muhimmanci har sai an samu sun shiga irin wadannan wuraren da ake bukatar su shiga.
“Kamar dai irin yadda muke ganin wadansu kananan hukumomi na yi wa mutanensu kuma ba za mu ce wadanda suka yi a baya ba su iya ba domin ita iyawa ai wani abu ne daban, hakan ne ta sanya a nan gaba kadan za mu fito da manufofinmu za kuma a bayyana su kowa ya gansu ya san su.
Akwai wani misali, ” kamar daga yankin jihohin Yarbawa misali kamar Legas sai kaga an bude wuri misali kamar yankin mazabar Saba don ji dan Shaba ne kuma a wannan mazabar ta Doka/Gabasawa na cike da wadansu muhimman manyan ma’aikatun Gwamnatin tarayya da wasu kuma masu zaman kansu sai mu nemi su dauki mutanenmu aiki domin yan mazabar mu muma mu samu gurbin aiki mu ci albarkacin zamansu a wannan wurin, za kuma ayi hakan ne tare da lallashi da lallaba, da ikon Allah ba wai da karfin mu ba mu same su mu zauna da su muga abin da za su ba mu na aiki daga cikin abin da Allah ya ba su na guraben aiki ko daga karami ko babban mataki, Insha Allahu.
THESHIELD Garkuwa