Daga Imrana Abdullahi
Dan takarar neman kujerar dan majalisar dattawa a yankin Shiyya ta daya cikin Jihar Kaduna Muhammed Mu’azu Mukaddas, ya bayyana yankin a matsayin wurin da ke cikin matsanancin Talaucin ayyukan raya kasa domin amfanin jama’ar yankin.
Muhammed Mukaddas ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan kammala tattaunawa da shugabannin jam’iyyar APC na jihar Kaduna a sakatariyar da ke cikin garin Kaduna.
Mu’azu Mukaddas ya ci gaba da bayanin cewa ya fito takarar neman jam’iyyar APC ta tsayar da shi ɗan takarar kujerar majalisar dattawa ne daga Shiyya ta daya a Jihar Kaduna, kasancewar yanki ne tamkar ba su da wakilci a majalisar dattawa domin ba wani aikin raya kasa da al’ummar za su ce daga dan majalisar dattawan yankin ya samar a halin yanzu ,saboda haka wuri ne kamar ba su da wakilci kowa a majalisar dattawan Najeriya.
Da yake mayar da jawabi bayan an yi masa tambaya ko me zai yi da zai bambanta da wanda ke kan kujerar a halin yanzu , Sai Mukaddas ya ce, ” kamar dai yadda kowa ya sani a dan kankanin lokacin da ya yi aiki a jihar Kaduna kowa ya ga irin ayyukan da ya samar na ci gaban al’umma da suka kai guda dari da Tamanin da Takwas wanda tuni jama’a na amfani da su a halin yanzu ba wai ba ne ba kuma za’ida ba ce abu ne a fili a bayyane, wanda hakan ne ya sa jama’a suka ce lallai sai na fito wannan takarar”.
“Tun jama’a na cewa in fito ina ja da baya har dai na mika wuya na fito wannan takarar a halin yanzu,wannan na daya daga cikin irin abubuwan da suka sanya jama’a suka ce sai lallai na tsaya wannnan takara domin a samu ingantaccen wakilci a majalisar dattawa ta kasa da zai wakilci shiyya ta daya”.
Ya kara da bayanin cewa ya zo ofishin jam’iyyar APC ne na Jihar Kaduna kamar yadda jagororin tafiyar ta sa suka umarta a zo a bayyana masu kudirin yin wannan takara domin wakiltar mazabar yankin Shiyya ta daya”.
” Kuma da yardar Allah idan muka kai ga ga ci kamar yadda na yi aiki a wadansu ma’aikatun Gwamnatin jihar Kaduna da na ta duniya baki daya zan ninka kokarin yin aikin da aka sanni da shi da ikon Allah don haka nake yin kira ga jama’a da su ba ni cikakken hadin kai da goyon baya ga yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu a samu wakilci da ba a taba samu ba a yankin Shiyya ta daya.
Sai Mukaddas ya kara da yin kira ga ya’yan jam’iyyar APC da su ci gaba da tsayawa a kan goyon Bayan jam’iyyar su da kuma bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani domin a samu nasarar da kowa ke bukata.
THESHIELD Garkuwa