Home / Big News / Shettima Yerima Ya Samu Kyakkyawar Tarba, Lale Da Marhabin Daga Shugabannin APC Na Jihar Kaduna

Shettima Yerima Ya Samu Kyakkyawar Tarba, Lale Da Marhabin Daga Shugabannin APC Na Jihar Kaduna

Daga Imrana Abdullahi
A ranar Talata ne 22 ga watan Afrilu, dan takarar da ke neman jam’iyyar APC ta tsayar da shi takarar neman kujerar majalisar dattawan Tarayyar Najeriya domin wakiltar mazabar tsakiyar jihar Kaduna Kwamared Shettima Yerima tare da tawagarsa ya kai ziyara ofishin jam’iyyar APC na Jihar Kaduna, inda wadansu daga cikin shugabannin tafiyar suka rika yin bayanin dalilin neman takarar da kuma irin muhimman kudirorin da dan takarar keda su idan Allah ya sa haka ta cimma ruwa.
A wajen shugabanni irin su Alhaji Dayyabu Mai Gwanjo, sun bayyana cewa sun zo NEMAN aure ne saboda haka suka zo wajen shugabannin jam’iyyar a matakin Jihar Kaduna domin su ne iyayen diyar da ake neman auren ta, musamman a muhimmanci irin na yankin tsakiyar Kaduna da ke zaman mazaunin hedkwatar arewacin Najeriya, domin garin Kaduna nan ne keda mazaunin gwamnatin Jiha don haka sai an samu jajirtaccen mutum mai kokari da aiki tukuru da zai ta shi a gaban majalisar dattawan ya na kare martaba tare da mikawa majalisar muradun jama’ar da yake wakilta.
Tun da farko, Alhaji Dangulguli ne ya fara gabatar da jawabi a kan irin makasudin zuwansu ofishin jam’iyyar a irin takarar da suke yi ta kujerar majalisar dattawan don haka muka zo wurin iyaye kuma shugabannin jam’iyyar APC na jiha.
Shima Alhaji Wada Garu, fadakar da jama’a ya yi cewa su dan takarar da suke tare da shi ba ruwansa da harkar da baya dace ba musamman ta fuskar matasa domin a duk iya saninsu da dan takarar su abin da suke Sani shi ne ya na kokarin inganta rayuwar matasa a kowa ne irin mataki, kuma matasan nan kasancewarsu Maza Ko Mata ne a cikin jama’a don haka duk inda ka ga matasa masu bin yan siyasa suna hargowa da ihu tare da wukake a tare da su sam ba a tare da wannan dan takara Shettima Yerima suke ba domin shi ba ruwansa da hakan burinsa shi ne dan kowa ya samu ilimin da ya dace da shi har ya zama abin da Allah ya tsara masa a cikin kyakkyawar rayuwa.
Suma mata ba a barsu a baya ba domin sun tofa albarkacin bakinsu inda suka yi wa mata albishir cewa kamar yadda a halin yanzu ake tafiya lallai Kwamared Shettima Usman Yerima ba zai mance da su ba, kamar dai yadda lamarin yake a halin yanzu komai sai da Mata.
A wurin wannan taron ziyarar ofishin jam’iyyar APC na Jihar Kaduna har da Matan zumunta na Kwaya da suka halarta kuma sun gabatar da rera wakoki da Kade kade inda suka kawatar tare da nishadantar da wurin
Dokta Bashir Sakataren Janar ne na tafiyar da Kwamared Shettima Yerima ke yin fafutukar Gwagwarmayar takara a karkashin ta ya yi wa dimbin jama’ar da suka taru a wajen taron ne da suka hada da shugabannin jam’iyyar APC na Jihar Kaduna cikakken jawabin waye Kwamared Shettima Usman Yerima.
Za kuma mu ci gaba da kawo maku irin yadda jawabai suka gudana a lokacin ziyarar da dan takarar neman jam’iyyar APC ta tsayar da shi neman kujerar majalisar dattawa domin wakiltar mazabar shiyya ta biyu a  Kaduna

About andiya

Check Also

Gwamnatin Zamfara Ta Yi Wa Masu Ƙaramin Ƙarfi 100 Auren Gata

  Gwamnatin Jihar Zamfara ta shirya tare da ɗaukar nauyin auren gata ga mutum 100 …

Leave a Reply

Your email address will not be published.