Home / Big News / Za Mu Ci Gaba Da Samar Da Romon Dimokuraɗiyya A Jihar Kogi – Isma’ila Isa

Za Mu Ci Gaba Da Samar Da Romon Dimokuraɗiyya A Jihar Kogi – Isma’ila Isa

Daga Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Kogi Ahmed Usman Ododo, ya bayyana kudirin Gwamnatinsa na ci gaba da samawa al’umma Romon Dimokuraɗiyyar,inda ya ce zai kara himma wajen samar da ayyukan da za su inganta rayuwar jama’ar Jihar.
Da yake gabatar da jawabin hakan mai bayar da shawara na musamman ga Gwamnan a kan harkokin yada labarai, Malam Isma’ila Isa, ya shaidawa manema labarai a Kaduna cewa  tuni Gwamnan tare da gwamnatin da yake yi wa jagoranci suka samu gagarumar nasarar yin ayyuka a muhimman bangarorin da suka shafi Lafiya,Ilimi tsaro da ayyukan bunkasa Rayuwar bil’adama.
Kamar yadda Isma’ila ya ce Gwamnatin Gwamna ODodo, ta kaddamar da Asibitocin samar da lafiya matakin farko har guda Tamanin (80) a fadin Jihar, kuma ana kara karfafa manyan Asibitocin Jihar ta hanyar samar da ma’aikata duk da nufin samawa jama’a hanyoyin inganta lafiya mai kyau.
Ya kara da cewa, Gwamnatin ta kara fadada  hanyoyin kula da lafiyar jama’a ta hanyar samar da inshorar lafiyar jama’a duk da nufin kara inganta hanyoyin kula da lafiyar jama’ar jihar.
A bangaren ilimin kuwa, Gwamnan ya taimakawa akalla yara sama da dubu Talatin (30,000) ya kuma gyara makarantun Gwamnati sama da dari Bakwai ( 700) domin kara inganta harkokin koyo da koyarwa a Jihar baki daya.
A bangaren samar wa da jama’a ababen more rayuwa kuwa, Isma’ila ya ce tuni an yi ayyukan samar da tituna a ƙalla masu nisan kilomita ashirin a dukkan kowace karamar hukuma guda 21 da ake da su a jihar da nufin kara bunkasa harkokin tattalin arziki a jihar kuma hakan zai bayar da damar kowace karamar hukuma ta hadu da yar uwarta a duk fadin jihar.
Ya kuma ci gaba da yin bayanin cewa Gwamnatin jihar ta samar da akalla fili mai fadin hekta dubu hudu (4000) da nufin samar da ingantaccen yanayin da masu zuba jari za su samu sukunin aiwatar da harkar zuba jari a Jihar
Game da batun magance matsalar tsaro a Jihar kuwa, mai taimakawa Gwamnan a kan harkokin yada labarai, cewa ya yi Gwamnatin Jihar Kogi karkashin Gwamna Usman ODodo, ta sayi jirage masu daukar hoto da kuma kai hari Duk domin taimakawa hukumomin jami’an tsaron da ke Jihar, an kuma kara inganta harkokin yan sintiri a jihar duk domin su taimakawa ayyukan jami’an tsaron da ke jihar”.
Ya kuma bayar da tabbacin irin karfi da nagartar jami’an tsaro a Jihar inda ya tabbatar da cewa hukumomin tsaron da ake da su za su magance matsalar tsaron a jihar.
“Babu wata shakka ko ko kwanto a kan hakan cewa za su yi maganin duk wata matsalar tsaron da ke cikin jihar, amma muna da karfin Gwiwar cewa jami’an tsaron da ke  Jihar sun fi karfin matsalar”, in ki Shi.
Gwamnatin kuma ta samar da motocin sufuri domin taimakawa ma’aikata ta hanyar samar da manyan motocin Bus Bus duk da nufin samar da sauki haka kuma an biya ma’aikatan kudin ariyas na albashi da sauran harkokinsu duk baki daya.

About andiya

Check Also

Croc-City 2026: When PR Met the Plough — Kaduna Declares War on Hunger With Words and Will

    By Zubair Abdurrauf Idris       For ten days, the ancient city …

Leave a Reply

Your email address will not be published.