Home / Labarai / Haɗarin Mota Ya Lakume Rayukan Mutane 9, 11 sun Jikkata A Yobe.

Haɗarin Mota Ya Lakume Rayukan Mutane 9, 11 sun Jikkata A Yobe.

 

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu 

 

Wani hadarin mota da aka yi da ya shafi wata mota kirar Golf da yara da ke dawowa daga gona a Kwarin Kwanta daura da hanyar Buni Gari-Bara a karamar hukumar Gujba cikin jihar Yobe, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane tara da suka hada da yara hudu tare da jikkatar mutane 11.

Wani ganau Mallam Abdullahi ya ce hatsarin ya faru ne a jiya da yamma inda motar da ke dauke da fasinjoji daga Damaturu zuwa Gulani ta kutsa cikin yaran da ke jiran abin hawa domin kai su gidajensu.

Abdullahi ya ce motar ta afkawa yaran ne a lokacin da take kokarin kaucewa ramuka.

Ya ce, “Lokacin da motar ta taka yaran, hudu sun mutu nan take, yayin da biyar daga cikin fasinjoji ciki har da direban suma suka mutu nan take.

“Wasu mutane 11 da suka samu raunuka daban-daban an kai su Asibitin kwararru, Buni-Yadi yayin da sauran kuma aka mika su Asibitin kwararru da ke Damaturu domin yi musu magani.

“Shugaban yaran Alaramma Bukar (BK) na Anguwar Danfulata na Buni-Gari wanda ba ya tare da su lokacin da lamarin ya faru shi ma yana kwance a asibiti sakamakon kidimar da ya yi kan faruwar wannan hadari kan daliban sa  Mun damu saboda adadin wadanda suka mutu a cikin yaran da suka jikkata na iya karuwa,” inji Majiyar

About andiya

Check Also

PRESIDENT TINUBU COMMENDS DANGOTE GROUP OVER NEW GANTRY PRICE OF DIESEL

  President Bola Tinubu commends the enterprising feat of Dangote Oil and Gas Limited in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.