Kasa da awanni 48 da rantsar da zababben gwamnan jihar Zamfara Dokta Dauda Lawal ya karbi takardun mika mulki a hukumance daga mataimakin gwamna mai barin gado Sanata Hassan Muhammad Nasiha wanda ya wakilci gwamna Bello Muhammad Matawalle mai barin gado.
Dauda Lawal ya samu rakiyar mataimakinsa Mani Malam Mudi a fadar gwamnati domin karbar takardun, Shugaban jam’iyyar PDP, Hon. Mukhtar Muhammad Luggage da sauransu
Cikakkun bayanai na zuwa nan gaba