Home / Big News / Zamu Ci Gaba Da Taimakawa Mata Da Matasa

Zamu Ci Gaba Da Taimakawa Mata Da Matasa

Daga Imrana Abdullahi
Honarabul Tahir Gambo Abubakar ya bayyana mata da cewa Kanne ne,Yayye ne, kuma mataye ne da suka kasance kashin bayan al’umma da gaba daya kowa ya san hakan don haka za’a ba su muhimmanci kwarai idan Allah ya kai mu gaci.
Honarabul Tahir Gambo ya kara da bayanin cewa  idan Allah ya amince ko a cikin manufofinmu duk za a ga batun Mata da Matasa a ciki da za a tabbatar da cewa Mata sun samu abin yi.
Tahir ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a Kaduna, inda ya ci gaba da bayanin cewa za a ga muhimman tsare – tsare n da za su inganta rayuwarsu kuma idan mun je majalisa za mu hada kai da mai girma Gwamna domin a cimma wannan manufa ta taimakawa mata, haka zalika suma matasa za mu tabbatar mun sama masu abubuwan da za su raba su da zaman banza kuma ana maganar atifishiyal intalijen ( AI) da kuma bayar da tallafi ba kuma na bayar da shinkafa kawai ba koda yake shima tallafin abinci ne, amma muna nufin Yadda za mu koya masu sana’o’i da za su zauna da kafar su a koda yaushe, sannan kuma maganar karatu nan ma za mu tabbatar da nemawa matasa maza da mata guraben karatu a makarantun Jami’o’i da kwalejin ilimin kimiyya da fasaha da dai sauran wadansu manyan makarantu domin matasa maza da mata su ci gaba da karatunsu bayan kammala karatun WEAC, NECO da sauran takardun shaidar kammala karatun Sakandare da makamantansu duk idan mun je majalisa za mu zauna da mai girma Gwamna mu gabatar masa da koken al’ummar mu kuma shima mutum ne mai son ya ga an magance duk wata matsala da ke cikin jama’a da ikon Allah.

About andiya

Check Also

Dangote, Pope Leo XIV, Trump, Xi Jinping, others Named in TIME 100 Most Influential People for 2026

  Renowned African industrialist and philanthropist, Aliko Dangote, has been named among TIME Magazine’s 100 …

Leave a Reply

Your email address will not be published.