Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gana da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a ranar Alhamis a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda suka tattauna muhimman batutuwan da suka shafi tsaro, tattalin arziƙi da kuma siyasar shekarar 2027.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa ganawar ta fi karkata ne kan halin tsaro a Zamfara, bunƙasar tattalin arziƙi, da kuma al’amuran siyasa da ke tafe.
Sanarwar ta nuna cewa, shugaban ƙasar ya sake jaddada ƙudirin Gwamnatin Yarayya na ƙara yawan sojoji da kuma samar da kayan aiki domin tabbatar da zaman lafiya a jihar Zamfara.
“Gwamna Lawal ya gudanar da ganawar sirri da Shugaba Tinubu jim kaɗan bayan shugaban ƙasar ya gana da gwamnonin jam’iyyar APC a Fadar Shugaban Ƙasa,” inji sanarwar.
An bayyana cewa tattaunawar ta mayar da hankali kan halin tsaro a Zamfara, inda aka yi duba kan nasarorin da aka samu zuwa yanzu, tare da gano wuraren da ke buƙatar ƙarin gyara domin tabbatar da dawo da cikakken zaman lafiya a faɗin jihar.
Shugaban ƙasar ya jaddada aniyarsa ta ba gwamnatin Zamfara cikakken goyon baya, ciki har da tura ƙarin sojoji da samar da muhimman kayan aiki domin sauƙaƙa ayyukan tsaro yadda ya kamata.
Haka kuma, Gwamna Lawal ya yi wa shugaban ƙasar bayani kan yadda tattalin arziƙin Zamfara ke bunƙasa, musamman ta fuskar ƙaruwa a kuɗaɗen shiga na cikin gida (IGR), inda suka tattauna hanyoyin da gwamnatin tarayya za ta ƙara taimakawa wajen bunƙasa masana’antu da samar da ayyukan yi.
Sanarwar ta ƙara da cewa, Shugaba Tinubu ya tabbatar da ci gaba da tallafin da gwamnatin tarayya ke bai wa Zamfara, tare da duba yiwuwar amfani da shirye-shirye da albarkatun gwamnati domin ƙarfafa masana’antu na cikin gida da samar da guraben ayyukan yi ga al’ummar jihar.
THESHIELD Garkuwa