Home / Big News / APC A Zamfara Ta Ayyana Cikakken Goyon Bayanta Ga Tinubu Da Dauda Lawal A Zaɓen 2027

APC A Zamfara Ta Ayyana Cikakken Goyon Bayanta Ga Tinubu Da Dauda Lawal A Zaɓen 2027

 

Jiga-jigan jam’iyyar APC a Jihar Zamfara sun bayyana cikakken goyon bayansu ga sake zaɓen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Dauda Lawal a babban zaɓen shekarar 2027.

 

 

An bayyana wannan matsaya ne a wani babban taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da aka gudanar a Gidan Gwamnati da ke Gusau a ranar Asabar, 25 ga Afrilu, 2026.

 

 

Taron ya haɗa manyan jiga-jigan APC daga sassa daban-daban na jihar, ciki har da tsofaffin gwamnoni huɗu, zababbun jami’ai, dattawa, wakilan matasa da mata, da sauran masu ruwa da tsaki daga ƙananan hukumomi 14 na jihar.

 

 

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Lawal ya bayyana cewa lokacin gudanar da irin wannan zama ya dace matuƙa, ganin yadda harkokin siyasa ke ƙara ƙarfi yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

 

 

Ya jaddada cewa sauya sheƙar da ya yi zuwa APC ba kawai siyasa ba ce, illa wata dabara ce ta ƙarfafa haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya domin inganta ci gaban Zamfara.

 

 

A cewarsa, shirin ceto na “Rescue Mission” da gwamnatinsa ke aiwatarwa na wakiltar muradin al’ummar jihar gaba ɗaya, ba na wata ƙungiya ko ɓangare kaɗai ba. Ya ƙara da cewa gwamnati na mai da hankali wajen dawo da zaman lafiya, gina cibiyoyi, da samar da ayyukan ci gaba da za su amfanar da jama’a.

 

 

Gwamnan ya kuma yi kira ga jiga-jigan jam’iyyar da su gudanar da harkokinsu cikin natsuwa da hikima, yana mai jaddada cewa siyasa na buƙatar sulhu, fahimtar juna da kuma yin aiki tare domin cimma manufa. Ya yi alƙawarin cewa adalci, gaskiya da bin ƙa’ida za su ci gaba da zama ginshiƙai a dukkan matakan tafiyar da jam’iyyar da gwamnati.

 

 

A nasu ɓangaren, tsofaffin gwamnoni da suka haɗa da Ahmed Sani Yarima, Mahmud Aliyu Shinkafi, Abdulaziz Yari da kuma Bello Mohammed Matawalle sun tabbatar da cikakken goyon bayansu ga jam’iyyar APC tare da marawa Tinubu da Lawal baya domin sake tsayawa takara a 2027.

 

 

Sanarwar taron da Ƙaramin Ministan Tsaro na Ƙasa, Matawalle, ya karanta ta bayyana cewa taron ya ba da dama wajen tattauna muhimman batutuwa da suka shafi haɗin kan jam’iyya, daidaita tafiyar gwamnati, matsalolin tsaro, da kuma shirye-shiryen tunkarar manyan zaɓukan gaba.

 

 

Taron ya kuma ƙarfafa buƙatar ci gaba da haɗin kai a tsakanin mambobin APC domin tabbatar da nasara a zaɓen 2027, tare da jaddada muhimmancin bin tsarin dimokuraɗiyya na cikin gida da kuma kauce wa duk wani abu da zai kawo rarrabuwar kai.

.

SULAIMAN BALA IDRIS
Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Zamfara
Afrilu 25, 2026

About andiya

Check Also

Ambassador Malami Shehu Ma’aji Mourns the Passing of Mr. Musa Ibrahim

      By Bashir Bello, Abuja   With profound sorrow and heartfelt sympathy, His …

Leave a Reply

Your email address will not be published.