Daga Imrana Abdullahi
Honarabul Tahir Gambo Abubakar, dan takarar neman kujerar majalisar dokokin Jihar Kaduna ne karkashin inuwar jam’iyyar APC daga Mazabar doka/Gabasawa a karamar hukumar Kaduna ta Arewa.
Honarabul Tahir Gambo Abubakar ya dai bayyana wannan aniyar ya sa ne a babban ofishin jam’iyyar APC na karamar hukumar Kaduna ta Arewa da ke kan titin Konsitution
Tahir Gambo Wanda ya isa ofishin jam’iyyar tare da dimbin magoya bayansa da suka yo tattaki a kasa tun daga Mazabar Shaba da ke cikin karamar hukumar domin ganawa tare da mika wa shugabannin jam’iyyar takardar da ke bayanin ana yin sha’awar takarar kamar dai irin yadda ka’idar jam’iyyar ta tanadar.
A wajen taron an gabatar da muhimman jawabai da dama da suka shafi batun tsayawa takarar Tahir Gambo Abubakar, da ake yi wa lakabi da raba gardama a tsakanin yan takara.
An dai yi ta yaba halayyar wannan dan takara Honarabul Tahir Gambo Abubakar, da kuma irin yadda yake rike da jama’a da suka hada da taimakon marayu da sauran marasa galihu da suke a cikin al’umma.
“Muna don mu nemi izini daga wurin jam’iyya domin a fita neman jama’a kafin lokacin zaben fitar da Gwani a cikin jam’iyya da muke fatan Allah ya ba mu Sa’a”.
Honarabul Tahir Gambo Abubakar ya kara da bayanin cewa a yau Talata 28 ga watan Afrilu, 2026 da na tsaya a gabanku domin neman albarka ne da neman taimako a wajen ku, Allah ya ba mu Sa’a da nasara, idan Allah ya amince shugabannin jam’iyya za su same ni mai Ladabi da biyayya za kuma a same ni mai hada kan jam’iyya.
“Duk abin da zai kawo mana hadin kai a cikin jam’iyya mai albarka shi ne ake nema,muna ta kokarin Allah ya sake dawo mana da Gwamna Uba Sani domin muna ji muna ganin irin ayyukan da ake yi a jiha domin rayuwar jama’a ta inganta.
Kuma kamar yadda mai girma babban dan siyasa ya fada Alhaji Hassan Jirgi ya fada wannan jam’iyya ta APC akwai abubuwan da ta yi tun daga can mataki na sama wato shugaban kasa har ga matakin karamar hukuma wanda an gani kowa ya shaida.
Tahir Gambo ya kuma ba jam’iyyar tabbacin cewa za su ci gaba da tallata jam’iyya a tafiyar da ake yi a halin yanzu, kuma za su tallata Gwamna Uba Sani da kuma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kuma hakan shi ne akida da kuma tafiyar baki daya.

Ya kuma yi wa shugabannin jam’iyyar alkawarin cewa za a ba su cikakken hadin kai da goyon baya a koda yaushe kasancewar mun ji akwai wata tsumagiya a gefen aljihu kuma za a yi amfani da ita da zarar an kauce ma hanya, don haka wannan tsumagiyar ya ce ya kawo ta wannan gidan don gaba daya iyayen sa ne.
Ya kuma yi godiya ga shugabannin Mazabu kasancewarsu matsayin iyaye.
“Akwai wani abu kadan da na yi Ni kadai da kashin kaina na kuma yada abin a kafafen sada zumunta da na labarai na ayyukan da Gwamna Uba Sani ya yi da suka hada da wuraren koyon sana’o’i da ya Gina da sauran dimbin ayyuka duk da nufin jama’a suga abin da Gwamna yake yi wa jama’a.
“Na fito ne domin muga irin yadda za a bayar da gudunmawa a taimakawa wannan jam’iyyar da kuma yadda za mu taimakawa al’ummar doka Gabasawa idan Allah ya yarda, shugaban jam’iyya ina godiya, ina godiya kwarai.

Daraktan Kamfe na tafiyar Honarabul Mustapha Zigogi, da kuma shugaban tafiyar baki daya Hassan Sale Jirgi duk kira suka yi da fadakarwa ga shugabannin jam’iyya da su bayar da damar ayi zaben fitar da dan takarar majalisar dokokin Doka/ Gabasawa a jihar Kaduna, wanda yin zaben zai taimaki jam’iyya kwarai.
A jawabinsa shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Kaduna ta Arewa, Honarabul Suleiman Wada Usman da ake yi wa lakabi da mai gidan sama kira ya yi ga ya’yan jam’iyyar musamman ma masu yin bayanai da korafe korafe na habaici, batanci a tsakanin ya’yan jam’iyyar wanda hakan kamar yadda ya bayyana ba zai taimaki rayuwar yan takarar da jam’iyyar ba ko kadan.
Wada ya ci gaba da bayanin cewa idan a wata rana kuma mutum na bukatar gyara wani da yake yin takara kuma fa ta yaya zai gyara shi bayan tun farko ya bata shi a kafafen sada zumunta.
THESHIELD Garkuwa