Related Articles
Imrana Abdullahi
Rundunar yan sanda ta kasa a Jihar Zamfara karkashin jagorancin kwamishinan yan Sanda Usman Nagoggo sun bayyana bankado sunayen wadansu manyan yan siyasa a gidan Matsafa.
Kwamishina Usman Nagoggo ya bayyana cewa sun samu nasarar bankado wannan gidan ne sakamakon bayanan sirrin da rundunar ta samu.
An dai gano sunayen manyan yan siyasa ne a rubuce, kuma bayanai sun bayyana cewa a duk lokacin da matsafan ke gudanar da lamarin masu za a ga kwari irin su Kadangaru da ire irinsu na mutuwa.