Mustapha Imrana Abdullahi Bayanan da muke samu daga Jihar Zamfara na cewa wadansu yan bindiga sun sace daliban makarantar koyon aikin Noma da ke garin Bakura. Kamar yadda rahotannin suka bayyana cewa dalibai Goma sha biyar (15) ne yan bindigar suka sace. Sai dai a wata majiyar da ba mu …
Read More »An Binne Wata Budurwa Da Ranta A Kafur
Daga Wakilin mu Bisa kuskuren da ya faru a wani gari da ke Kafur cikin karamar hukumar Kafur a Jihar Katsina, rahotanni sun bayyana cewa an yi kuskuren binne wata budurwar da ake tsammanin ta mutu. Sa’adatu Hassan Kafur, ta samu matsalar ta ba wutar lantarki ne wanda sakamakon hakan …
Read More »An Tabbatar Da Gaskiya, Adalci A Jihar Kaduna – Shehu Bakauye
Mustapha Imrana Abdullahi Dan majalisar wakilai ta tarayyar mai wakiltar kananan hukumomin Giwa da Birnin Gwari, honarabul Shehu Balarabe da ake yi wa lakabi da Bakauye, ya bayyana cewa a iya saninsa an tabbatar da yin zabe cikin gaskiya da adalci a zaben shugabannin mazabu a Jihar Kaduna. Honarabul Shehu …
Read More »Gwamna El-Rufai Ya Yi Tir Da Harin A Kauru
Mustapha Imrana Abdullahi Gwamna Malam Nasiru El- Rufa’I ya yi Tir da Allah wadai da kakkausar murya da harin da aka kai a ranar Litinin a wasu kauyuka a karamar hukumar Kauru. Kauyukan sun hada da Unguwar Magaji, Kigam,Kisico da Kikobo duk a cikin karamar hukumar Kauru a Jihar Kaduna. …
Read More »Mahaifiyar Sminu Alan Waka Ta Rasu
Mustapha Imrana Abdullahi Mahaifiyar Aminu Abubakar da aka fi Sani da Alan waka ta rasu ta na da shekaru 70 a duniya. Mahaifiyar Alan Waka mai suna Hajiya Bilkisu Sharif Adam ta rasu ta na da shekaru 70 a duniya ta kuma bar yaya biyu da jikoki 25. Kuma kamar …
Read More »Hukumar Zabe Ta Dage Zabe A Kaduna
Mustapha Imrana Abdullahi Hukumar Zaben kananan hukumomi ma8 zaman kanta a Jihar Kaduna ta sanar da dage zaben kananan hukumomi zuwa ranar 4 ga watan Satumba,2021. Shugabar hukumar Dokta Saratu Binta Dikko – Audu ce ta sanar da hakan a wajen taron masu ruwa da tsaki a kan harkokin zaben, …
Read More »Daya Daga Cikin Masu Zaben Sarki Na Masarautar Zazzau Sani Aliyu Ya Rasu
Mustapha Imrana Abdullahi Wani fitacce daga cikin masu zaben Sarki a masarautar Zazzau, Limamin Konan Zazzau Malam Sani Aliyu ya rasu. A cikin wata takardar sanarwar da ke dauke da sa hannun mai magana da yawun masarautar Abdullahi Aliyu Kwarbai, ta bayyana rasuwar Limamin a daren yau Alhamis. “Allah …
Read More »Shugabannin Arewa Ne Matsalar Yankin – Gwamna Matawalle
Daga Imrana Abdullahi Gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, ya bayyana a fili a wajen wani babban taron Shekara shekara na kungiyar marubuta a kafofin yada labarai mai su na ( Arewa Media Writers) da aka yi a garin Kaduna cewa shugabannin arewa ke da alhakin matsalar tsaron da ya …
Read More »Yan Bindiga Sun Sace Sarki Kpop Ham Mai Daraja Ta Daya
Mustapha Imrana Abdullahi Rahotannin da muke samun a halin yanzu daga Jihar Kaduna na cewa yan bindiga sun sace wani Sarki mai daraja ta daya Kpop Ham, Dokta Jonathan Danladi Gyet Maude (JP, OON) wanda sanannen Sarki ne kuma jagoran al’ummar Jaba cikin Jihar Kaduna. Rahotannin da muke samu na …
Read More »Gwamna Matawalle Zai Gabatar Da Jawabi A Wajen Taron Matasa A Kan Harkar Tsaro
 Imrana Abdullahi Gwamnan Jihar Zamfara Bello Muhammad Mutawalle zai gabatar da kasida a game da kalubalen tsaro, ci gaban Siyasa yadda lamarin ya shafi arewacin Nijeriya. Zai gabatar da jawabin ne a babban taron marubuta a kafafen yada labarai na arewacin Najeriya da za a yi a ranar Lahadi …
Read More »